Monday, May 25, 2026
HomeNewsTSAKANIN MALAM WAKKALA DA SANATA YARIMA

TSAKANIN MALAM WAKKALA DA SANATA YARIMA

By: Abubakar Sadeeq

 

Ga duk mai bibiyar siyasar jihar Zamfara, ya san cewa yanayin siyasa ya dumama sosai a ‘yan kwanakin nan da Jam’iyyar APC wadda ta ke mulki a jihar ta fitar da Jadawalin zaben fitar da gwanaye da zasu tsaya mata takara a zaben 2019 da yake tunkarowa. Wannan dumamar yanayi ya sanya jama’a da yawa rudewa da tunanin makomar jihar gaba daya idan aka samu kuskure wajen tsayar da ‘yan takarar da basu cancanta ba.

 

Senator Ahmad Sani Yarima, kamar yadda al’amar Zamfarawa suka sani har yanzu shi ne yak e binsu bashi ba don komai ba sai don dumbin alheri da kuma cigaba da ya samarwa jihar a lokacin da yayi mulkin Jihar na shekara Takwas wanda tunda ya bar gwamnati basu samu irin sa ba. Bayan haka Yarima ya kasance uba ga Talakawan jihar gaba daya, ba don komai ba sai don sauraron koke-kokensu da yake yi da kuma maganta musu matsalolinsu dai dai karfinsa. A duk lokacin da zaku zauna hira da Maigirma Sanata Yarima ba shi da zance da ya wuce yaya za’a a samu cigaba a jihar Zamfara?

 

Maigirma Mataimakin Gwamna Malam Ibrahim Wakkala, ya kasance mutum mai nagarta da jin kan talakawa da son cigaban jihar Zamfara, haka kuma kowa ya tabbatar da cewa Malam Wakkala mutum ne mai cikakkiyar biyayya ga nagaba da shi, idan muka duba baya zamu ga cewa biyayyar da yake yiwa Sanata Yarima ce ta saka ya bar mukamin da Gwamna Mamuda Shinkafi ya bashi saboda gwamnatin ta sauka daga kan turbar da Yarima ya dorata, Malam Wakkala ya bar mukaminsa ya bi Maigirma Yarima sunyi aiki dashi a majilisar tarayya. Haka kuma tunda aka tabbatar da shi a matsayin abokin takarar Maigirma Abdul-aziz yari ya bayar da gudunmawarsa da biyayyarsa dari-bisa-dari domin cigaba jihar, wannan ya sanya Maigirma Shetimman Mafara Gwamna Abdul-aziz Yari bai taba ambatar rana guda da Malam Ibrahim Wakkala ya saba mas aba ko kuma yayi wani abu wand aba daidai ba. Kasancewar Gwamna Abdul-aziz ya na da yawan tafiye-tafiye, Malam Wakkala yakan kwashe wata shidda bai fita daga Jihar Zamfara ba, ba don komai sai don ya saurari talakawa ya kuma tabbatar da tsaro a daukacin Jiha baki daya.

 

Kamar yadda sanarwa ta fito cewa Maigirma Sanata Yarima zai Jagoranci tawagar al’ummar Zamfarawa wajen sayawa Malam Ibrahim Wakkala Fom na tsayawa Takarar Gwamnan Jihar Zamfara a Zaben 2019 da yake zuwa, ya nuna cewa Sanata Yarima yana wakiltar Talakawan Jihar Zamfara ne domin sayan Fom din domin shine dan takarar da ya fi cancanta ya zama Gwamna Jihar. Ta tabbata dai Gwaman Abdul-aziz Yari bayaso mataimakin na say a gajeshi  ko menene dalilinsa? al’ummar jihar su kuma suna son Malam saboda kaunarsu da yake yi da sheremusu hawaye. Allah ya tabbatar da Alherinsa!

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

FOLLOW US:

6,985FansLike
1,458FollowersFollow
553SubscribersSubscribe

Most Popular