Daga garin Bauchi
Dubban masoya wasan polo daga sassa daban-daban na Najeriya da ma ƙasashen waje sun ci gaba da cika filin wasan Col. A.D. Umar Polo Ground da ke Bauchi domin shaida wasannin rana ta uku na Gasar Bauchi Polo 2026. Gasar ta ci gaba da jan hankalin manyan ‘yan wasa, masu sha’awar polo da baƙi daga ciki da wajen ƙasar.
A cikin hotunan, an ga yadda ƙungiyoyi daban-daban suka fafata cikin ƙwarewa da jarumtaka, lamarin da ya kayatar da dubban masu kallo da suka halarta. Gasar na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan bukukuwan wasanni da ke haɗa al’umma tare da bunƙasa harkokin yawon buɗe ido da tattalin arzikin Jihar Bauchi.
📸 Hoto: Labari Daga Bauchi Media
