Daga Muazu Hardawa, Bauchi
Ganin yadda mata ke samun matsalar cutar mahaifa a lokacin da suka girma ko idan sun zo haifuwa ake wahala, gidauniyar Alhaji Ali Usman Foundation ta himmatu wajen bayar da taimakon allurar rigakafi cutar bakin mahaifa kyauta wa yara mata Yan Shekara tara zuwa 14 a Yankin Toro.
Gidauniyar ta gudanar da wannan gagarumin aiki a garin Magama Gari da ke karamar hukumar Toro jihar Bauchi cikin makon da ya wuce.
A yayin wannan aiki an wayar da kan iyaye mata kan wannan matsalar kuma sama da Yan mata Dari suka karbi allurar da kuma ilmantuwa kan matsalar cutar.
Kwamared Yusuf Aliyu Fada shugaban kungiyar maaikatan kiwon lafiya na sa kai masu bayar da Agaji kyauta shine ya jagoranci gangamin allurar da wayar da kan iyaye mata don samun nasarar shirin.
Yadda cikin jawabinsa Kwamared Aliyu Fada ya bayyana cewa muhimmin abin da suke yi shine wayar da Kai da kuma bayar da allurar wacce idan za a biya a kasuwa kowace allurar ana kashe naira dubu 30.
Amma Alhaji Alli Usman ya saya kuma ya bayar don taimako a matsayin sa na Dan kasa Mai kishi, Kuma tsohon ma’aikacin gwamnatin da ke son ganin lafiyar mutanen sa ta inganta.
Malama Khadijat Abdulkadir da Malama Munirata Aliyu Jibrin na cikin maaikatan da suka gudanar da aikin, inda cikin jawabinsu suka Yaba tare da bayyana cewa aikin ya taimaka kuma da.fatar za a ci gaba da yiwa Alhaji Aliyu Usman godiya da adduah.
Kuma ya.kamata mutane suci ci gaba da masa adduah Allah ya ba shi ikon taimaka wa kan sauran cututtuka. Da fata masu hannu da shuni za su rika gudanar da irin wannan aikin don taimakon marasa karfi.
Malama Habiba Magama da Hajara Yakubu da Binta da Ummi Musa da Amina wasu mata iyayen da suka bayar da yaran su don karbar allurar rigakafin cutar bakin mahaifar, cikin jawabinsu suka godewa Alhaji Ali Usman, saboda daukar dawainiyar shirin allurar yadda suka gode masa tare da jan hankalin iyaye su lura da lafiyar yaran su ta hanyar zuwa asibiti a kan lokaci idan an ji matsala game da lafiya.
Malam Abdullahi Munkaila Mai unguwar Magama Gari cikin jawabinsa ya godewa Wanda suka gudanar da aikin da Wanda ya dauki nauyin Shirin . Haka kuma ya ja hankalin Yan siyasa da masu hannu da shuni su rika tallafawa masu karamin karfi saboda ganin yadda matsalar tattalin arziki ke sa mutane cikin wahala da kuma mutuwa saboda rashin kudin jinya da sayen magani.
Don haka ya yi farin ciki kuma ya godewa Wanda suka Yi aikin da wanda ya bayar da dukiyar sa don taimakon matan Yankin.
Dangadiman Bauchi Hakimin Jama’a Alhaji Bala Sulaiman a Yankin Toro ya karbi ziyarar tawagar jami’an kiwon lafiya da suka gudanar da aikin kuma ya godewa Alhaji Ali Usman ya yi fatar ya fadada aikin taimakon zuwa fannin ilmi da tallafi Kai aikin gona, saboda akwai iyaye talakawan da yaran su ke da kokari amma basu da Halin taimaka musu su je manyan makarantu don haka suke zama a gida tarbiyyar su na lalacewa.
Hakimin Jama’a Alhaji Bala Sulaiman ya ce kofarsa a Bude take a duk lokacin da ake bukatar taimakon su ko neman shawara kada a ji nauyi a same su a shirye suke wajen bayar da dukkan goyon bayan da ake bukata.
Don haka ya bukaci a isar da godiya ga Wanda ya dauki nauyin shin wato Alhaji Ali Usman Foundation kuna suna masa adduah da fata Allah ya ba shi Halin ci gaba da wannan aikin taimaka wa masu karamin karfi.
