Sunday, April 14, 2024
HomeHausaƙungiyar masu kafafen yaɗa labarai ta Arewacin Najeriya ta Karrama Asma'u Sadiq

ƙungiyar masu kafafen yaɗa labarai ta Arewacin Najeriya ta Karrama Asma’u Sadiq

A Daren lahadin da ta gabata ne ƙungiyar masu kafafen yaɗa labarai ta Arewacin Najeriya ta karrama fitacciyar mawakiyar gada wato Asma’u Sadiq (Baby Nice) saboda gudunmawar da take bayarwa a sana’arta ta waka. Alh. Abdullahi Yalwa Ajiyan Yawuri, wanda shine shugaban ƙungiyar , ya ce, ƙara buɗe kafafen yaɗa labarai kan ƙara samar da ci gaba a tsakanin al’umma.

Ajiyan Yawuri ya bayyana hakan ne, a yayin taron liyafar cin abinci da girmama wasu daga cikin kafafen yaɗa labarai da kuma wasu mawaƙa a Arewacin Najeriya, wanda ya gudana a ɗakin taro na Dabo TV Centre dake kan titin Jami ar Bayero ta Kano.

Asma’u Sadik wadda aka fi sani da (Baby Nice) ta godewa Allah da samun wannan karramawa, sannan ta yi wa wannan kungiya fatan alheri akan dukkan ayyukansu.

Asma’u Sadik (Baby Nice) shahararriyar mawakiyar gada, kuma yanzu haka itace, shugabar sashin shirye-shiryen tashar Dala FM Kano,

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

FOLLOW US:

6,985FansLike
1,458FollowersFollow
553SubscribersSubscribe

Most Popular