Tuesday, July 16, 2024
HomeHausaDutse: An Bukaci Mata da su dawo da Awakin da aka tallafa...

Dutse: An Bukaci Mata da su dawo da Awakin da aka tallafa musu domin a bawa wasu

Daga Garba Abdullahi Bagwai

An bukaci Matan da suka amfana da rancen awaki a karkashin shirin bada rancen awaki na gwamnatin jihar Jigawa a yankin karamar hukumar Dutse su hanzarta dawo da awakin da aka basu domin wasu Matan su amfana.
Shugaban kwamatin rabawa da dawo da rancen awakin na jihar Jigawa, Dakta Salisu Abdullahi ya yi wannan bukatar lokacin da kwamatin ya ziyarci mazabun yankin domin karbo awakin da aka rabawa Mata rance.
Dakta Salisu Abdullahi ya ce gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya bullo da shirin ne domin bunkasa tattalin arzikin Matan jihar nan, musamman mazauna yankunan Karkara bisa wa’adin shekaru biyu na dawo da awakin da aka basu rance.
A sakon da ta aike ga taron karbo rancen awakin, shugabar Mata ta jam’iyyar APC ta karamart hukumar Dutse, Hajiya Binta Hudu a madadin Matan da suka ci gajiyar shirin ta godewa gwamna Muhammad Badaru Abubakar bisa bullo da shirin bada rancen awakin da kuma samarwa Mata hanyoyin sana’oin dogaro da kai.
A nasa jawabin shugaban sashen aikin gona na karamar hukumar Dutse, Malam Mamuda Abdu ya shawarci Matan da har yanzu basu dawo da rancen awakin ba, su hanzarta dawo da su domin takwarorin su su samu damar samun rancen.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

FOLLOW US:

6,985FansLike
1,458FollowersFollow
553SubscribersSubscribe

Most Popular