Friday, December 20, 2024
HomeHausaTsaro: Karamar hukumar Garki ta dau matakin lura da zirga-zirgar bakin Fulani

Tsaro: Karamar hukumar Garki ta dau matakin lura da zirga-zirgar bakin Fulani

Daga Garba Abdullahi Bagwai

Karamar hukumar Garki ta kafa kwamitin sa-ido domin lura da zirga-zirgar bakin Fulani makiyaya da suke shiga yankin daga kasashen ketare.
Shugaban karamar hukumar, Alhaji Mudassir Musa Garki wanda ya bayyana haka a lokacin taron kwaimtin tsaro na yankin, yace an kafa kwamitin domin daukar matakan hana rigingimu tsakanin Fulani makiyaya da manoma.
Yace aikin wakilan kwamitin ne sa-ido tare da sanar da jamian tsaro da zarar sun gab akin Fulani makiyaya, inda yayi kira ga alummar yankin su guji daukar doka a hannunsu.
Alhaji Mudassir Musa Garki yace karamar hukumar tana daukar matakai daban daban domin tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a fadin yankin.
A halin yanzu kuma shugaban karamar hukumar Garki yayi kira ga alummar yankin da basuyi rijistar zabe ba hanzarta zuwa cibiyoyin da aka ware domin yin rijistar. Alhaji Mudassir Musa ya umarci aknsiloli da masu bada shawara su fadakar da alumma muhimmancin mallakar katin zabe da katin

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

FOLLOW US:

6,985FansLike
1,458FollowersFollow
553SubscribersSubscribe

Most Popular