Monday, July 22, 2024
HomeHausaAn Nada Shugaban Asibitin Best Choice Jakadan Zaman Lafiya na Duniya

An Nada Shugaban Asibitin Best Choice Jakadan Zaman Lafiya na Duniya

Shugaban asibitin kwararru Best Choice Hospital da kuma Bestmedix pharmacy, Kano, wato, Alh. Auwal Muhammad Lawal ya samu lambar yabo ta fitaccen jakadan zaman lafiya ta kungiyar masu rajin tabbatar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya.

Lawal ya sami Kyautar ta Chartered Fellowship ne a matsayin sa na 1556 don karramawa ga me da gudunmawar da yake bayar wa ga jama’arsa na kusa, na kasa da kuma na duniya baki daya.

A cewar sanarwar hukumar, Ambasada Per Stafsen, JP, MP World Peace President, Denmark International Association of World Peace Advocates, Auwal, ya cancanci duk hakkoki da gata da ke kungiyar, kuma ana sa ran zai yi aiki a matsayin mai samar da zaman lafiya a kowane bangare na duniya dangane da ayyana haƙƙin mutane na samun zaman lafiya (1984) na ƙudurin Majalisar Ɗinkin Duniya.

Auwal Muhammad Lawal, an haife shi a unguwar Gwale Quarters, karamar hukumar Gwale Kano.

Alh Auwal a matsayinsa na dan kasuwa yana da imanin taimakon jama’a da kasuwanci tun yana karami.

Lawal ya girma tare da iyaye masu daraja kuma yan kasuwanci da tawali’u, suna ba shi ƙarfin hali don yin koyi da abin da yake gani a daga iyayensa.

Muhammad, yana da sha’awar karfafa matasa ta hanyar samar da ayyukan yi da jagoranci. Kasancewar shi C.E.O kuma mai kula da harkokin kasuwanci da dama da kuma daukar ma’aikata, ya shaida sha’awarsa na kawar da rashin aikin yi da matasa da kuma bala’o’i na tabarbarewar tarbiyya a tsakanin al’umma.

Auwal Lawal attajiri ne, mai daraja bil’adama da kuma tausayawa a al amuransa.

A kullum yana kokarinsa wajen taimakonsa ga mabukata da marasa galihu a cikin al’umma.

A matsayinsa na gwarzon ci gaban al’umma, ko yaushe yana tuntuɓar ƙungiyoyin jama’a don tallafawa da kuma taimakawa ƙoƙarin da ake buƙata don ɗaukaka masu bukata.

Alh Auwalu shi ne C.E.O kuma shugaban kamfanin Grand Choice Bureau De-change Wuse Zone 4 Abuja, da Best Choice Specialist Hospital No 488 sabuwar Gandu Quarters, Kumbotso Local Government sai kuma Best Medix 24hrs Pharmacy and store No 529 Gadon Kaya Quarters Kano City.

Alh Auwalu mutum ne da ba shi da girman kai, wanda za a iya tabbatar da kishin bil’adama da kuma tabbatar da shi a duk harkokinsa na kasuwanci da ayyukan alheri.

Ya kasance bisa la’akari da irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban al’umma;

Hakazalika Hakimin garin Garo na karamar hukumar Kabo ne ya zabe shi aka nada shi sarautar gargajiya a matsayin Danmalikin Garo.

Alfijr.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

FOLLOW US:

6,985FansLike
1,458FollowersFollow
553SubscribersSubscribe

Most Popular