by Kabiru Getso
Shugaban Kwalejin kimiyya da Fasaha ta Tarayya dake Kazaure (Husaini Adamu Federal Poly Technique Kazaure) Dr Sabo Wada Dutse ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da manema labarai.
Yace babu shakka wajibi ne matasa dama iyayen matasan su bada himma wajen koyan Sana’ar dogaro da kai komai kankantarta musammanan a wannan halin da ake ciki na karancin guraben ayyuka a Gwamnatoci.
Dr Sabo ya Kara da cewar hakan ne yasa Kwalejin ta himmatu wajen samar da kwasa kwasai da kuma kayayyakin koyar da Sana’oin hannu domin inganta rayuwar Daliban kwalejin dama sauran al’umma.
Kazalika Dr Sabo yayi kira da masu rike da madafun iko dama sauran al’umma musamman masu hannu da shuni da su cigaba da hobbasa wajen tallafawa harkar ilimin matasa domin shine hanyar da za’a samu saukin rashin tsaro da kuma rashin aikin yi da ya addabi matasa.
Bugu da kari ya ja hankalin dalibai da suyi aiki tukuru wajen neman ilimi tare da koyan Sana’a yadda ya kamata don taimakawa kansu dama sauran al’umma baki daya.