Daga Garba Abdullahi Bagwai
Karamar hukumar Garki ta kafa kwamitin sa-ido domin lura da zirga-zirgar bakin Fulani makiyaya da suke shiga yankin daga kasashen ketare.
Shugaban karamar hukumar, Alhaji Mudassir Musa Garki wanda ya bayyana haka a lokacin taron kwaimtin tsaro na yankin, yace an kafa kwamitin domin daukar matakan hana rigingimu tsakanin Fulani makiyaya da manoma.
Yace aikin wakilan kwamitin ne sa-ido tare da sanar da jamian tsaro da zarar sun gab akin Fulani makiyaya, inda yayi kira ga al
ummar yankin su guji daukar doka a hannunsu.
Alhaji Mudassir Musa Garki yace karamar hukumar tana daukar matakai daban daban domin tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a fadin yankin.
A halin yanzu kuma shugaban karamar hukumar Garki yayi kira ga alummar yankin da basuyi rijistar zabe ba hanzarta zuwa cibiyoyin da aka ware domin yin rijistar. Alhaji Mudassir Musa ya umarci aknsiloli da masu bada shawara su fadakar da al
umma muhimmancin mallakar katin zabe da katin