Daga Aminu Dahiru
A shirye – shiryen babban taro na masu ruwa da tsaki akan harkar Gas da za’a gudanar a garin Kano a karkashin Jagorancin kamfanin GACN wato Gas Aggregation Company Nigeria da tallafin gwamnatin Jihar Kano, sun shirya bikin al’adun gargajiya wanda aka yi a dakin taro na THE AFFICENT da ke layin Magaji Rumfa a cikin garin Kano.
Bikin ya samu halartar manya manyan baki daga ciki da wajen kasar nan, musamman ma Jihohin Kogi, Nassarawa, Niger da kuma Kaduna saboda shi babban Taron da za’ayi ranar Alhamis 29 ga watan Yuli 2021 za’a yi shi ne domin fito babban amfanin aikin bututun Gas na AKK wanda ya shafi wadannan jihohi guda 4 har da Jihar Kano cikonsu ta biyar ta fannin cigaban tattalin arziki.
Shahararrun makada da masu wasanni iri iri daga wadannan jihohi biyar sun yi wasannin masu kayatarwa. Haka kuma an kawo abinci kala kala na gargajiya daga su alawar madara zuwa su iloka da su waina da sauransu.
Daga karshe babban Darakta Kamfanin GACN Mr. Lekan ya godewa mahalarta bikin al’adun gargajiyar da kuma fatan zasu fito ranar babban taron domin halartarsa, sannan kuma yayi addu’ar kowa ya isa gida lafiya. An gama taro da misalin karfe 9 na dare