Friday, April 26, 2024
HomeHealthZamfara: Matawalle ya nada Yusuf Idris Daraktan Yada Labaransa

Zamfara: Matawalle ya nada Yusuf Idris Daraktan Yada Labaransa

Ibrahim Bello Gusau Ibg

Mai girma gwamnan jahar zamfara, Hon. Bello Muhammad (Matawallen Maradun), ya aminta da nada Yusuf Idris a matsayin direktan yada labarai na ofishin sa.

Kafin nadin shi, Yusuf Idris, direktan yada labarai ne a ofishin tsohon mataimakin gwamnan jaha Malam Ibrahim Wakkala Muhammad kuma kwararren danjarida ne da ya dade a cikin wannan aiki na jarida.

A madadin daukacin magoya bayan G8, muna mi ka kyakykyawar godiyar mu ta musamman ga mai girma sabon gwamnan jahar zamfara, Hon. Bello Muhammad (Matawallen Maradun) akan wannan karamci.

Haka zakika muna taya sabon direktan yada labarai na mai girma sabon gwamna samun wannan mukami, da fatar Allah ya sa a wanye lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

FOLLOW US:

6,985FansLike
1,458FollowersFollow
553SubscribersSubscribe

Most Popular