Thursday, May 16, 2024
HomeHausaTsarin Taimakekeniyar Lafiya, tsari ne na Addinin Musulunci - Dr.Bashir Aliyu Umar

Tsarin Taimakekeniyar Lafiya, tsari ne na Addinin Musulunci – Dr.Bashir Aliyu Umar

A ziyarar Fahimtar juna da Hukumar Taimakekeniyar Lafiya ta Jihar Kano ta kaiwa Babban Limamin Masallacin Al-Furqan Dr. Bashir Aliyu Umar da ke unguwar Nassarawa GRA a satin da ya wuce, ya yi matukar farin ciki da ziyarar da hukumar ta ka wo ma sa, haka kuma ya ji dadin bayanan da aka yi masa wanda ya yanke hukuncin hukumar ta sake dawowa a lokacin yin Tafsir na Al-Qur’ani ai Girma domin yi wa al’umma bayani domin amfa nuwa gaba daya.

A ziyarar ta biyu a lokacin yin baya nan, Dr. Abdullahi Sa’ad wanda ya ke shi ne Daraktan shirye-shirye a hukumar yayi cikakken bayani akan cewa akwai tsare-tsare dabam-dabam wanda ya hada da na Ma’aikatan Gwamnati, ‘yan Pansho; Tsarin “yan kasuwa, Tsarin Ma’aikatan Kamfanunuwa masu zaman kansu, Tsarin Dalibai da dai sauransu. Dr. Abdullahi ya cigaba da bayani cewa akwai tsari da ke kira Vital wato tsarin masu hannu da shuni shine mutum zai biya N12,000 sannan ya zabi Asibitin da ya ke so, na gwamnati ko na ‘yan kasuwa da suke cikin tsarin domin samun kulawa da lafiyar sa daga matakin farko (Primary Care) har zuwa gaba wato (Secondary Care) a na fa ta ma nan gaba zai iya zama har (Tertiary Care) har zuwa shekara guda.

Bugu da kari Likitan ya cigaba da ce wa wannan tsarin ya yi daidai daabun da malamai su ke kira Waqaf wato masu hali da suke ajiye kudi ma su yawa domin kula da wani abu har zuwa wani lokaci, a nan mutum ya na iya zuwa hukumar ya kawo kudinsa ya fadi adadin mutanen da ya keso a yi wa Rijista domin kula da lafiyarsu har tsahon shekara daya, a Asibitocin da suke kusa dasu da suke cikin tsarin.

Daga karshe Dr. Abdullahi ya yi kira ga duk mai neman karin bayani, zai iya zuwa Ofishin Hukumar kai tsaye da ke Gida mai Lamba 27A da ke Titin Sokoto Road ku koma ya kira labar wayoyin da suke jikin Takardun da aka rarraba; Haka kuma ya yi addu’a da fatan Alkhairi ga Babban Liman da ya bayar da wannan dama da aka yi al’umma bayani.

Babban Liman Dr. Bashir Aliyu Umar ya yi cikakken sharhi akan baya nan da akayi, in da ya ke cewa hakika Gwamnatin Jihar Kano ta yi babban tunani wajen kirkiro da wannan Hukuma, ya cigaba da cewa tsahon lokaci tun lokacin ya na kwamishina a Hukumar Shari’a ta Jihar Kano su ke tat tunanin yaya za’ayi a samu irin wannan tsarin da zai maye gurbin NHIS wanda shi tsari ne na jari hujja. Dr. Bashirya cigaba da cewa wannan tsarin taimakekeniya ba wani abu ba ne illa tsarin ‘Takaful’ tsari ne da mai karfi ke taimakawa ma ra karfi ballanta na kuma kula da lafiya ya zama wajibi a addinin musulunci, Malam ya cigaba a inda yayi kira da masu arziki cewa ga tsari da zaka saka kudin ka, ka samu lada kan lada; sannan ya cigaba da kawo kissoshin abubuwa na taimakekeniya da su ka faru tun lokacin sahabbai da kuma amfanin yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

FOLLOW US:

6,985FansLike
1,458FollowersFollow
553SubscribersSubscribe

Most Popular