Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yabawa Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Cif Nyesom Wike, kan ci gaban ayyukan gine-ginen ababen more rayuwa da ake gudanarwa a Babban Birnin Tarayya.
Shugaba Tinubu ya yi wannan yabon ne a ranar Alhamis yayin ƙaddamar da gadar musayar hanya (Interchange) da ke mahadar Titin Arterial Road N16 da Ring Road 11, wadda ta haɗa Gundumar Jahi da Gundumar Gwarinpa a FCT.
Tinubu, wanda Shugaban Majalisar Dattawa, sanata Godswill Akpabio, ya wakilta a wajen taron, ya ce ababen more rayuwa su ne ginshiƙin ci gaba da wadata. Ya kuma yaba wa Wike da tawagarsa a FCT bisa aiwatar da manufofin Renewed Hope Agenda na gwamnatinsa.
A cikin wata sanarwa da Mataimaki na Musamman kan Yaɗa Labarai da Sadarwa ga Shugaban Majalisar Dattawa, Anietie Ekong, ya fitar, an ambato Shugaban Ƙasar yana cewa:
“Bari na yaba wa Ministan FCT mai ƙwazo, Barrista Nyesom Wike, CON. Wike, kana aiki tuƙuru. Ka ɗauki umarnina na ‘ka sa Abuja ta yi aiki yadda ya kamata,’ kuma kana aiwatar da shi yadda ya dace.
“Daga tituna zuwa gadoji, daga tsakiyar birni zuwa garuruwan da ke kewaye da shi, kana yaɗa manufar Renewed Hope a faɗin FCT. ‘Yan Najeriya suna gani, kuma mazauna yankin suna jin amfaninsa a rayuwarsu ta yau da kullum. Allah ya ƙara basira.”
Shugaban Ƙasar ya tuna irin wahalhalun da matafiya ke sha a wannan hanya kafin a gina gadar.
Ya ce: “Wannan mahadar hanya ta kasance tana haddasa cunkoso sosai. Layin ababen hawa yana tashi daga Maitama zuwa Gishiri, daga Jahi zuwa Gwarinpa. Ana ɓata sa’o’i masu yawa, ana ƙona mai a banza, harkokin kasuwanci suna jinkiri. Amma daga yau wannan matsala ta zo ƙarshe.
“Wannan gada ta buɗe muhimman sassan FCT tare da haɗa su cikin sauƙi da sauran yankunan Babban Birnin Tarayya. Kayayyaki za su riƙa isa cikin sauri, ma’aikata za su koma gida da wuri, ɗalibai za su isa makaranta akan lokaci, kuma tsaro zai inganta saboda masu aikata laifi kan fi samun damar aikata laifi idan cunkoson ababen hawa ya tsaya cak.”
Shugaban Ƙasar ya gode wa al’ummar Jahi, Gwarinpa, Katampe da sauran yankunan da ke makwabtaka da su saboda haƙurin da suka yi yayin da aka karkatar da zirga-zirga saboda aikin ginin. Ya kuma buƙace su da su ɗauki aikin a matsayin nasu tare da kare kayayyakin gwamnati daga lalata su.
Tun da farko, Ministan FCT ya bayyana cewa gwamnatin da ta gabata ce ta bayar da kwangilar gina wannan gadar musayar hanya, kwanaki biyu kafin ta sauka daga mulki.
Ya ce bisa umarnin Shugaban Ƙasa na bai wa manyan ayyukan da aka gada muhimmanci tare da kammala su, an hanzarta aikin har aka kammala shi domin amfanin al’umma.
