Tuesday, October 29, 2024
HomeHausaTallafi: Dangote ya Kaddamar da Rabon Tallafin Shinkafa Buhu Miliyan Daya a...

Tallafi: Dangote ya Kaddamar da Rabon Tallafin Shinkafa Buhu Miliyan Daya a Garin Kano

Gidauniyar Aliko Dangote ta kaddamar da aikin fara raba buhunhunan shinkafa mai nauyin kilograms 10 sama da miliyan daya ga al’ummar Najeriya farawa da jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya.

A lokacin da ya kaddamar da aikin fara raba buhunhunan shinkafar ga mutane da ke zama masu rauni a cikin al’umma, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa wannan wani bangare ne na irin ayyukan da suke na tallafawa al’umma da daukar nauyi don su rage radadi da ake fuskanta a wannan lokaci da ya zo kuma a lokacin watan Ramadhana mai falala.

“ A wannan rana da muka fara wannan tafiya ta jinkai da ba da hadin da kai mun hadu a nan don kaddamar da aikin rarraba shinkafa mai nauyin kilogiram 10 sama da miliyan daya ga mutanen da ke zama masu rauni a cikin al’umma, inda za mu rarraba a kananan hukumomi 774, wannan zai sa mu kashe sama da Naira miliyan dubu 15.”

A cewar Dangote za a fara raba shinkafar da jihar Kano da Legas wacce Kanon za ta samu buhu 120,000.
Shugabar sashen kasuwanci a kamfanin na Dangote Hajiya Fatima Dangote tace sun fara wannan rabo da jihar ta Kano ne saboda ita ce mahaifar su.
Shi kuwa Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya yaba da tsarin da Gidauniyar ta Dangote ta zo da shi inda za ta yi amfani da dakarun Hisbah don tabbatar da ganin tallafin ya kai ga wadanda suka kamata a bawa.
“Dama burinmu kenan mu tabbatar da ganin wadanda aka yi abin dominsu sun amfana.”

Wasu da suka samu tallafin cikin masu bukata ta musamman sun bayana wa Muryar Najeriya yadda suka ji da wannan tallafi.
“Wallahi mu kam sai san barka Allah Ya saka wa Dangote alkhairi Allah Ya raba shi da mahaifiyarsa lafiya. Wannan taimako ya samu farinciki matuka mu da iyalanmu.”

VON

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

FOLLOW US:

6,985FansLike
1,458FollowersFollow
553SubscribersSubscribe

Most Popular