Monday, July 22, 2024
HomeHausaƘUNGIYAR ACF TA YI KIRA DA A ƘARA TATTAUNAWA AKAN RIKICIN ƘASAR...

ƘUNGIYAR ACF TA YI KIRA DA A ƘARA TATTAUNAWA AKAN RIKICIN ƘASAR NIJAR

ƘUNGIYAR ACF TA YI KIRA DA A ƘARA TATTAUNAWA AKAN RIKICIN ƘASAR NIJAR DA ƊAGE TAKUNKUMAN TATTALIN ARZIKI DA AKA SAKA MUSU, TARE DA YABAWA SANATOCI BISA ƘIN AMINCEWA DA KAI HARIN SOJI

Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Mutanen Arewa wato Arewa Consultative Forum (ACF) ta yi kira da a ɗage takunkumin da Shugaban Ƙasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu da Ƙungiyar ECOWAS suka ƙaƙabawa Jamhuriyar Nijar. Haka kuma tana neman ƙarin tattaunawa da hukumar sojin ƙasar domin kiyaye ƙara samun matsaya ta tattaunawa, bayan ƙarewar wa’adin mako guda da aka baiwa gwamnatin ƙasar na maido da mulkin dimokuraɗiyya a kasar.

Mu a ACF muna ƙara yin Allah wadai da juyin mulkin da aka gudanar a Jamhuriyar Nijar tare da neman kare lafiyar shugaba Mohamed Bazoum da na mambobin gwamnatinsa daga waɗanda suka yi juyin mulki.

Najeriya da Nijar suna hulɗar ƴan uwantaka a tsawon shekaru aru-aru, mu kuma a matsayin mu na Ƙungiyar ACF a yayin da muka yi nazari a kan sabbin matsalolin siyasa da ya kunno kai a ƙasar Nijar, takunkumin tattalin arziki da kuma ƙarewar wa’adin mako guda da aka bai wa gwamnatin mulkin soja a Nijar, Ƙungiyar mu ta cimma matsayar cewa Tattaunawar dai ita ce mafi a’ala da kyawun zaɓi don kaucewa aukuwar mummunan rikici ko matsala tsakanin ƙasashen biyu da yankin yammacin Afirka baki ɗaya. Ya kamata mu yi amfani da duk wani abin da ake buƙata na maslaha, diflomasiyya, siyasa, tattalin arziki da kuma masu faɗa a ji, don dawowa da al’umar Ƙasar Nijar martaba da walwalar su, waɗanda a tarihi suka ɗauki Najeriya a matsayin Babbar Yaya!

A wannan gaɓar, domin kawo ƙarshen wannan matsalar mun fitar da matsayar mu tare da bada waɗannan shawarwari kamar haka:

  1. ACF ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Ƙungiyar ECOWAS da su sake duba lamarin tare da maido da cikakkiyar tattaunawa da gwamnatin mulkin sojan Nijar ta hanyar ɗage takunkumin tattalin arziki da sauran takunkuman da aka ƙaƙabawa kasar nan take a matsayin wata alama ta fatan alheri don samun damar tattaunawa cikin gaggawa.
  2. Muna kira ga Shugaba Tinubu da Ƙungiyar ECOWAS da su sake duba hanyoyin da suke bi na tunkarar rikicin ƙasar Nijar bisa haƙiƙanin gaskiya da suka haɗa da cewa galibin ƙasashen da ke kewaye da jamhuriyar Nijar ba mambobin Ƙungiyar ECOWAS bane, ma’ana basa yankin Yammacin Afirka, kamar yadda Aljeriya, Libya da Chadi na iya kallon kai hare-haren soja kamar ayyana yaƙi ne a kan iyakokinsu. A yayin da kuma hukumomin ƙasashen Mali da Burkina Faso da kuma Guinea a ɗaya ɓangaren suka bayyana goyon bayansu ga jagororin juyin mulkin Nijar, lamarin na buƙatar taka-tsantsan, domin kada a ƙara tayar da zaune tsaye a yankin yammacin Afirka.
  3. Ƙungiyar ACF ta yabawa Ƙungiyar Sanatocin Arewa bisa kyakkyawan aikin da suka yi wajen ganin sun shawo kan takwarorinsu a majalisar dattawa, inda suka yi watsi da amfani da ƙarfi kai tsaye ga Jamhuriyar Nijar a ƙoƙarin su na ganin an dawo da mulkin dimokuraɗiyya a ƙasar Nijar. Muna godiya ta musamman ga babban zauren Majalisar Dattawa na ƙasa kan yadda suka bi hanyar masalaha da lumana don warware rikicin da ka iya munana.
  4. Muna kira da babbar murya ga gwamnatinmu da ta ƙara himma wajen ƙara amfani da matakan lumana, siyasa da diflomasiyya don nemo bakin zaren warware wannan matsala. Don haka, muna son gwamnatin Najeriya ta duba waɗannan batutuwa: i) Maidowa da Jamhuriyar Nijar wutar lantarki ba tare da ɓata lokaci ba; ii) Buɗe dukkanin iyakokinmu da ƙasar ta Nijar da kuma ba da damar shige da ficen al’umar ƙasashen biyu da kuma kayayyaki tsakanin ƙasashen biyu zuwa Najeriya; da iii) Dakatar da duk wani takunkumi da aka ƙaƙabawa ƙasar ta Nijar domin bin umarnin da ƙungiyoyin ECOWAS, AU, ko wata hukuma/ƙasa ta yi.
  5. Muna kuma yabawa shugaban ƙasa Bola Tinubu kan taron da ya yi da gwamnonin Sokoto, Kebbi, Yobe, Katsina, Jigawa da dai sauran waɗanda ke da iyaka da jamhuriyar Nijar kamar yadda ACF ke neman ya cigaba da tuntuɓar masu faɗa a ji, a ciki da wajen Najeriya, gabanin sabon taron shugabannin ƙasashen ƙungiyar ECOWAS da za a yi a ranar Alhamis mai zuwa.

A ƙarshe kungiyar ta ACF tana nanata kira ga Ƙungiyar ECOWAS da sauran ƙasashen duniya da cewa dole ne su buƙaci a bawa shugabannin da suka jagoranci juyin mulki taƙaitaccen wa’adi ko lokacin da za su miƙa ko mayar da mulki ga zaɓaɓɓun shugabannin jamhuriyar Nijar. Har ila yau, ƙasar Najeriya da ma daukaciny hukumomin shugabannin ƙasashe mambobin Ƙungiyar ECOWAS, dole ne su fara ɗaukan irin matakan da zai sa a daina yi musu kallon suna yi ne don neman kuɗi neman kuɗi ko sun zama karnukan farauta turawan yamma.

Sa hannu:

Farfesa Tukur Muhammad-Baba,
Sakataren Yaɗa Labarai,
Haɗaɗɗiyar kungiyar Mutanen Arewa (ACF)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

FOLLOW US:

6,985FansLike
1,458FollowersFollow
553SubscribersSubscribe

Most Popular