Friday, April 12, 2024
HomeHausaMaryam Shetty : Ina Baka san Gari ba, Saurari Daka

Maryam Shetty : Ina Baka san Gari ba, Saurari Daka

DAGA Fatuhu Mustafa

Nayi mamaki da wasu suke zancen Maryam Shettima ba yar Kano ba ce, wasu nasal har ga Allah ba su san ta ba ne, domin da yawan su ko dai ba a haife su a 90s ba, ko kuma suna yara lokacin, zuwa 2000. Akwai kuma wadanda tsananin hassada ce kawai, sun sani sarai cikakkiyar yar Kano ce. Saboda haka muka yanke shawarar mu gaya muku wacece ita a Kano.

Daga bangaren mahaifinta dai ta fito ne daga zuriyar Shettimawan Kano. Mun kuwa san kakanninta tun daga Shettima Shekare zuw Shettima Ibrahim dukkan su Kanawa ne usul. Mun kuma san Alhaji Yakubu Kado da kuma irin alakar da ke tsakanin su da Sarkin Kano Bayero. Haka kuma kawunta wan mahaifin ta, ya tsayawa NPN takarar gwamna a Kano a zaben 1979, wato Alhaji Ibrahim El Yakub. Wani kawun na ta, barrister Ali el Yakub, shi ne kwamishinan sharia mafi dadewa a Kano, domin ya yi kwamishinan sharia da kusan dukkanin gwamnonin soja da suka zauna a Kano illa kalilan. Sannan yayanta wanda aka fi sani da Kosasshe ya rike mukamin minista a zamanin gwamnatin Buhari da ta shude. Dukkanin wadannan daga danginta suke, to ta yaya ita ba za ta zama yar Kano ba. Ban kawo batun wan mahaifin ta Alhaji Ubale Minjibir da Alhaji Aminu Miniibir ba. Amma dukkannin wadannan aka kalla ake batun ita ba yar Kano ba ce!

Daga bangaren mahaifiyar ta kuwa, Maryam jikar Malam Amadu Rufai ce, wani malamin makaranta tun zamanin turawa, da yayi aiki a Kano. Malam Amadu Rufai, asalin sa mutumin Daura ne, da aka turo shi Kano, yayi aikin koyarwa a makarantar middle. Saboda irin kwazon sa, da dattakon sa, sai Sarkin Kano Bayero ya aura masa daya daga cikin yayan sa, wacce aka fi sani da Nanin Daura (Allah ya jikan ta). Wannan aure ne aka haifi mahaifiyar Maigirma Minista Hajiya Maryam Ibrahim Shettima. Ita kuma ita ce Allah ya hada ta aure da Malam Ibrahim Minjibir suka haifi Hajiya Maryam.

Ta ko ina aka duba, Hajiya Maryam cikakkiyar yar Kano ce, ba kuma ta bukatar amincewa ko yardar wani, domin Allah da kan sa ya amince mata ya kaddaro aka haife ta a Kano.

Haka kuma Hajiya Maryam, a sanin da nayi mata, ko shakka babu, bana zaton za ta gaza kai banten ta. Nayi imanin Kanawa ko mutanen Arewa ba za su yi da na sanin bata wannan mukamin ba.

Muna fatan Allah ya rika mata, ya zamar mata jagora.

.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

FOLLOW US:

6,985FansLike
1,458FollowersFollow
553SubscribersSubscribe

Most Popular