Daga Abubakar Sadiq
Kamar yadda ta saba a yau Asabar, 16 ga watan Afrilu 2022, kungiyar hadinkai da zumunci ta rabawa marayu Dari da Hamsin (150) kayan masarufin Azumi a unguwanni biyar na jihar Kano, unguwannin sun hada da Tukuntawa Bakin Dogo, Sabuwar Gandu, Gyadi Gyadi Farin Masallaci, Tishama da kuma Walalambe.
Bikin rabon tallafin wanda ya samu halartar jigajigan kungiyar karkashin jagorancin Alh. Abdussalam Kayarima, akwai Manbobi da suka hada da Maigirma Sadukin Gumel, Dr. Ibrahim Muhammad Gandu, Sarkin Shanun Toron Bade, Alh. Umar Zakari, Comred Isma’il, Alh Bello Madobi, Hajiya Ruqayya Adado, Hauwa’u Abdulmalik Fulani, Ummukulsum Garba Sulaima da kuma PRO Baba Balarabe, A jawabinsa da ya gabatar a wajen bikin tallafin Alh. Kayarima ya godewa duk Manbobin kungiyar da suka samu damar halartar bikin sannan ya jawo hankalinsu akan a cigaba da bayar da hadin kai musammam wajen biyan kudin wata wata, saboda da irin su ne aka har ha da, da kuma kudin da aka samu a gidauniyar da aka kafa wanda jimlar kudin yakai kusan Naira Dubu Dari Takwas. Shugaban ya kara da cewa bayan sallah kungiyar Hadinkai da Zumunci (HKZ) za ta yi wani sabon shiri na ‘yanto ‘yan gidan yari ta hanyar biya musu tara.
Daya daga cikin Marayun da su ka samu tallafin Halima Sulaiman dake unguwar Walalanbe ta nuna matukar farin ciki da wannan tallafi da ta samu Taliya, Shinkafa da kuma Man girki, ta yi addu’a ga kungiya akan Allah ya dauka ka ta.
Daga karshe PRO Baba Balarabe yayi addu’a ga Allah ya mayar da kowa gidajensu lafiya.