Wednesday, May 29, 2024
HomeHausa2023: Hon. Bashir Ahmad ya kai ziyarar Goyon bayan Tsayawa Takara, Karamar...

2023: Hon. Bashir Ahmad ya kai ziyarar Goyon bayan Tsayawa Takara, Karamar Hukumar Albasu

Daga Abubakar Sadiq

A yau wannann rana ta Juma’a 15th 4, 2022 tawagar Mal. Bashir Ahmad, mataimaki na musamman ga Shugaba Muhammadu Buhari kan kafafen sadarwa na zamani takai ziyarar girmamawa ga al’ummar Albasu.

Ziyarar ta fara ne da ofishin shugaban Karamar Hukumar Albasu Alh. Mu’azu Abubakar Gagarane (Dan sarki) don bayyana masa da jama’ar sa takara tare da neman goyon bayansa da al’ummarsa ta Albasu don sahalewar su ga Mal. Bashir Ahmad ya zama Dan Majalisar tarayya mai wakiltar kananan Hukumomin Gaya, Ajingi da Albasu a kakar zabe mai zuwa ta 2023. Karkashin jam’iyar

Daga bisani muka rankaya kai ziyara ga fadar uban kasa ga Kananan hukumomi 3 na kasar Gaya tun asali, Makaman Gaya, Hakimin Albasu Dan Majalisar Sarkin Gaya, daya daga cikin masu zaɓar Sarki a masarautar Gaya Alh. Bashir Albasu domin ya sanya Albarka tare da adu’a’oi ga Mal. Bashir kan abun da yake nema na Dan Majalisar tarayya a matsayin na uba ga al’umma.

Ziyarar bata tsaya anan ba, mun kai ziyarori wure dabam dabam don jaje da ta’aziya ga al’umma ta Albasu, tare gashshe – gashshen ga jama’a don bayyana takara a 2023.

Allah ya bamu sa’a.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

FOLLOW US:

6,985FansLike
1,458FollowersFollow
553SubscribersSubscribe

Most Popular