By Kabiru Getso
Shugaban karamar hukumar Ungwaggo Engr Dr Abdullahi Garba Ramat ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa yace Tuni shiri yayi nisa wajen tafiyar da shugabancin karamar hukumar akan tsarin fasahar zamani.
Ramat ya Kara da cewar tun a shekaru da dama da suka wuce ya kamata ace tuni shuwagabanni sunyi nisa wajen aiwatar da wannan tsari,domin samun saukin kawar da duk wasu matsalolin da suka addabi al’umma musamman sha’anin matsalar tsaro.
Ya kara da cewar su yanzu a karamar hukumar Ungoggo tuni sunyi nisa wajen maida duk wasu al’amura a tsarin fasahar zamani,domin hatta takardar shaidar zama cikakken dan karamar hukuma Ana samar da ita ne ta yanar Gizo.
Baya da tarin nasarori da karamar hukumar ta samu a fannin tsaro akwai wata babbar Nasara ta tsarin biyar kudin haraji a kananan injinan musayar hada hadar kudade na Zamani wanda wannan wani tsari ne da zai taimakawa Shuwagabannin dama al’umma baki daya.
Kazalika Shugaban karamar hukumar ta Ungoggo ya ja hankalin Matasa da Su maida hankali wajen Samar da Nagartattun Shuwagabannin a mataki daban daban dake fadin kasarnan. Domim yanzu lokaci yayi da matasa zasu farka su shiga Sahun neman Guraben Shugabanci domin suma a dama da su a sha’anin cigaban kasar nan.
Ya kara da cewar babu shakka yayi imani akwai rawar da matasa zasu taka a lamarin jagorancin kasar nan. Don haka ya zama wajibi su tashi tsaye wajen tabbatar da cancantar fitar da duk wani wakili da zai wakilci al’umma a matakai daban daban dake fadin kasar nan.
Alhamdulillah Daman Ai shugaba kuma jagora ya chanchanchi fiye da haka duba da irin kyakkywar aniyarsa ga alummah…….
Allah yaimaka sanatan kano ta tsakiya…