Wednesday, May 29, 2024
HomeHausaGwamnatin Jigawa za ta bayar da kwangilar sanya sabbin kayayyakin kiwon lafiya...

Gwamnatin Jigawa za ta bayar da kwangilar sanya sabbin kayayyakin kiwon lafiya a wasu Asibitoci

Daga Garba Abdullahi Bagwai

Ma’aiktar lafiya ta jihar Jigawa ta bude tayin bada kwangilar samarwa da kuma sanya sabbin kayayyakin kiwon lafiya irin na zamani ga sabbin manyan asibitocin garuruwan Gantsa da Garki da kuma Guri.
Da yake bude bada tayin kwangilar babban Sakataren ma’aikatar, Dakta Salisu Mu’azu ya shaidawa masu nema kwamgilar cewa gabatar da mafi kankantar farashi, ba ya na nuna cancanta ko dacewar samun kwangilar ba ne.
Babban Sakataren, ya ce babbar bukatar dai ita ce kwarewa da kamfani yake da shi wajen gudanar da aiki.
Dakta Salisu Mu’azu ya kara da cewa bayan tallata tayin bada kwangilar, daga bisani tawagar kwararru za ta duba cancanta da kuma ka’idojin da suke kunshe a dokokin saye da samar da kayayyaki na Hukumar tantance ayyukan kwangila ta Jihar Jigawa.
Da yake jawabi a madadin kamfanonin da suka nemi kwangilar, wakilin Kamfanin Maiwuya Construction Company, Malam Abdullahi Nafi’u ya yabawa Gwamnatin Jiha da ma’aikatar saboda basu wannan dama.
Kamfanoni uku ne suka nuna sha’awar basu kwangilar.
Kamfanonin sune Maiwuya Construction Company da Dagara Integrated Sevices Limited da kuma Babban Doki General Enterprises.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

FOLLOW US:

6,985FansLike
1,458FollowersFollow
553SubscribersSubscribe

Most Popular