Saturday, October 24, 2020
Home Hausa Tsakanin Gwamna Yari da Kogunan Gusau

Tsakanin Gwamna Yari da Kogunan Gusau

Daga Abubakar Sadeeq

Ga duk wananda ya ke bibiyar siyasar jihar Zamfara ya san da cewa akwai tambarwar siyasa da take faruwa tsakanin Gwamna da kuma ‘Yan takarar gwaman jihar a karkarshin jam’iyyar APC su 8 wanda suka hada da Maigirma Mataimakin Gwamnan Jihar wato Malam (Dr) Ibrahim Wakkala da Sanata Kabiru Marafa, Ministan Tsaro, Alh Dauda Lawan Dare da sauranasu. Wannan dambarwar siyasa ta samo asali ne daga lokacin da Gwamna Yari ya tara mukarrabansa a gidan gwamnati ya fito da jadawalin sunayen ‘yan takararsa a matsayin wai anyi sulhu, bayan bai tuntubi ‘yan takarar ba, a lokacin ne ya ambato Mukhtar Shehu Idris a Matsayin Dan takararsa na Gwamna ba tare da lura da abun da talakawan garin suke so ba, haka kuma ba tare da tunanin cigaban jihar ba.

Hakika tun daga wannan lokaci mutane su ke tambayar wai shin me ye lafin Mataimakin Gwamna Malam Ibrahim Wakkala da Gwamna ya ha na shi takarar? Haka ma sauran ‘yan takarar, kamar su Marafa ko Dauda ko Mamuda da sauransu, amma idan ka duba sai ka ga babu wanda ya ke da wani tabo da zai hana shi takarar Gwamna Jihar. Wannan shi ya sa idan ka tambayi kanka wai me yasa Gwamna Yari ya dauko Koguna ya ce shine Dan takararsa? Amsar dai bata wuce ace shine Kwamishinansa na Kudi ba amma babu wata kwarewa ta musamman da zaka ce ya fi sauran ‘yan takarar ba, to me yasa Gwamna Yari ya ce ko sama da kasa zata hade sai Koguna ya zama Dan takara? Amsar dai ba zata wuce a ce kasancewar Koguna shine Kwamishinan Kudi ya zama lallai ya na tartare da sirrin Gwamna Yari gaba daya wanda ya hada da kudaden Jihar Zamfara da aka barnatar wajen hidimar Neman Auren ‘yar Shugaban Kasa wanda ba’ayi ba, haka kuma kudaden da ake zurarewa da sunan gina Jami’ar Jihar a Mafara da kuma kudaden da ake ta yawon duniya da ba’a zama a Jihar Zamfara domin magance matsalar tsaro dadai sauransu.

A tunanin Gwamna Yari idan Koguna ya zama Gwamnan Zamfara zai cigaba da rufa masa asiri akan badakalar da ya tafka a zamanin mulkinsa wanda a ganina ya makaro, domin Hausawa na cewa ‘Maganin ka da ayi, to ka da a fara’ indai ka ci nanun to nanun dole ta ci ka, tunda ya Debi kudin Jama’a to sai ya biya su.

Ragowar ‘yan takarar gwamna da aka fi sa ni da G8, saboda kishinsu da Jihar Zamfara ya sa suka dauri aniyar sai anyi adalci kuma sai an bawa talakawa zabin da su ke so, shine ya kawo matakan da suka dauka na ankarar da Uwar Jam’iyya ta kasa da kuma zuwa kotu domin kotu tayi hukunci. Hakika duk da kudin da gwamna Yari ya ke ta zubarwa wajen bayar da cin hanci ga alkalai amma har yanzu Allah bai bashi nasara ba saboda gaskiya daya ce, daga bayan nan ma ta tabbata ya bawa alkalan kotun daukaka kara ta Sokoto cin hancin Dala Miliyan Uku $3m domin suyi hukuncin da zai yi masa daidai, sai gashi asiri ya tonu, alkalan sun zare hannunsu daga shari’ar.

Wani abu mai matukar tayar da hankali shine kalaman da Gwamna Yari yayi na cewa idan babu ‘yan takarar APC a zaben 2019 to lallai ba za’a yi zabe kwatakwata a Jihar Zamfara ba, wannan kalaman tunzuri ne da zasu iya kawo mummunan tashin hankali kuma daga bakin Gwamna. A gaskiya yana da matukar muhimmanci ga Dattawan Jihar da su jawo hankalin Gwamna akan wannan kalaman nasa domin ya janye su domin zaman lafiyar garin baki daya.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

FOLLOW US:

6,985FansLike
1,458FollowersFollow
553SubscribersSubscribe

Most Popular

Contracts below N5bn will no longer be awarded to foreign firms -FG

The federal government has directed that contracts below N5 billion will no longer be awarded to foreign firms. This...

IGP ordered withdraws policemen attached to VIPs

The Inspector-General of Police, Mohammed Adamu, has ordered the withdrawal of all police officers attached to all VIPs across the nation with...

Curfew: Flight Operations at MM Airport Lagos suspended

Flight operations at the Murtala Mohammed Airport in Lagos have been suspended following the 24-hour curfew imposed in the state by Babajide...

#EndSARS: Senate asks Buhari to address Nigerians

The Senate on Tuesday asked the President, Major General Muhammadu Buhari (retd.), to address the nation immediately on the current nationwide protests...