Sunday, April 19, 2026
HomeNewsAlaka ta yi Tsami Tsakanin Gwamna Yari da Shugaban kasa Muhammad Buhari

Alaka ta yi Tsami Tsakanin Gwamna Yari da Shugaban kasa Muhammad Buhari

Daga Abubakar Sadeeq

 

Ajiya ne Gwabnonin Jam’iyyar APC suka je fadar shugaban kasa Muhammad Buhari domin ta ya shi murnar tabbatar wa da aka yi masa Na zama Dan Takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar APC a Babban taron Jam’iyyar da ya gabata a karshe satin da ya wuce a garin Abuja.

Gwamnonin sun isa fadar Shugaban kasar ne a karkashin jagoranci maigirma Gwamnan  Jihar Imo wato Rocas Okorocha wanda shine Shugaban kungiyar Gwamnoni ‘yan Jam’iyyar APC, ga wani abun mamaki Sai gashi babu Gwamna Abudulaziz Yari a cikin wadan su ka samu damar hallarta, duk da cewar taro ne mai matukar muhimmanci baya da cewar shine ya ke shugabantar kungiyar Gwamnoni ta kasa baki daya.

Hakika wannan ziyara tayi dadai da lokacin da hukumar zabe ta aikewa uwar Jam’iyyar APC akan cewa su sani basu da ‘yan takara ko guda a wannan zaben da za’ayi Na 2019 kasancewar jami’ansu sun basu rahoton cewa ba’ayi zaben Primaries ko daya ba a Jihar Zamfara, duk da cewar Gwamna Yari ya kira taron manema labari karanta sunayen ‘yan Takarar da ya ke so ya na ikirarin cewa anyi zaben Primaries a Jihar.

Sanin kowane cewa shugaba Buhari baya goyon bayan zalunci da kuma son kai, kuma ba ya goyon bayan Abdulaziz Yari akan abun da yayi na kokari kawo rashin nasarar Jam’iyyar APC a Zamfara.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

FOLLOW US:

6,985FansLike
1,458FollowersFollow
553SubscribersSubscribe

Most Popular