Monday, December 23, 2024
HomeHausaAn kaddamar da Sabon Shugabancin kungiyar Zurgazurgar sufiri a Jihar Kano

An kaddamar da Sabon Shugabancin kungiyar Zurgazurgar sufiri a Jihar Kano

Daga Kabiru Getso

Kwamishinan Ayyuka na jihar Kano Engr Idris Garba ya kaddamar da kungiyar zurgazurgar Sufuri reshe jihar kano tare da bude masu sabon ofishi a harabar ma’aikatar ayyuka.

Engr idris Garba ya bayyana cewa sufuri na da matukar muhimmanci ga rayuwar al’umma hakan yasa Gwamnatin jihar kano karkashin Shugabancin Dr Abdullahi Umar Ganduje a shirye suke domin bada gudummuwar da duk ya kamata don ha6aka sufuri a jihar Kano.

Shima a nasa jawabin sabon Shugaban zurgazurgar ababan hawa na jihar kano Alh Lawan Isah Bubaram ya bayyan gansuwarsa akan yadda Gwamnati ke bada kulawa ta musamman akan harkar sufuri,kana yayi Kira ga sauran al’umma da su cigaba da bada cikakken hadin Kai akan sha’anin Sufuri.

Lawan Isah Baburam ya sha alwashin bin matakan da duk ya kamata domin ciyar da wannan kungiya gaba, tare da bijiro sabbun dabaru dobin farfado da kungiyar tayi gogayya da sauran takwarorinta na jihoshi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

FOLLOW US:

6,985FansLike
1,458FollowersFollow
553SubscribersSubscribe

Most Popular