Daga Kabiru Getso
Hadaddiyar Kungiyar Ma’aikatan Lafiya ta kasa Reshen Jihar Kano JOHESU ta zabi Sabon Shugabanta a Kano
Com Ibrahim Muhammad Maikarfi Shine ya lashe zaben da aka gudanar jiya a sakatariyar kungiyar dake cikin Birnin Kano.
Comrade Makarfi kafin za6ensa shine Shugaban kungiyar ma’aikatan jinya da Unguwar zoma na jihar kano Wato Nursing and Midwifery Association Of Nigeria.
Maikarfi ya Godewa Allah bisa wannan dama da ‘ya’yan kungiyar suka bashi na jagorantarsu,kana yasha Alwashin cigaba da jajircewa wajen ciyar da kungiyar gaba.
Kazalika yayi kira da wadanda suka nemi wannan matsayi basu samu ba da su cigaba da bada tasu gudummuwar wajen ciyar da kungiyar gaba.