Data Abba Anwar
Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yi tir da Allah Wadai ga ‘yan Kwankwasiyyar PDP wadanda su ka kai farmaki ga wasu ‘yan jam’iyyar APC wadanda su ka shirya wata addu’a ta musamman ta rokon Allah neman zaman lafiya a zabubbukan da ke tafe a wannan kasa.
Wanda a dalilin wannan farmaki ne da ‘yan Kwankwasiyyar su ka kai har wasu su ka rasa rayukansu. Wasu kuma su ka samu raunuka daban-daban. Abin takaici da nuna rashin mutunci.
Wannan rashin kyautawa da ta’annatin da su ka yi sun yi shine a kan idon jagoransu Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda su ke kewayen kamfen din su na siyasa na yakin neman zabe.
Sannan ga su dauke da makamai tsirararsu lokacin da su ka kai farmaki kan masu addu’a wacce wakilin Kiru da Bebeji a majalisar tarayya, Abdulmumini Jibrin Kofa ya shirya, a na rokon Allah kan samun zaman lafiya da kwanciyar hankali. Musamman a lokutan zaben da ke tafe.
Wannan farmaki da ta’annati shine na baya-bayan nan da ‘yan Kwankwasiyya ke kai wa jama’a haka kawai wai saboda su kawo cikas idan lokacin zaben ya zo. Tun yanzu sun fara hangowa kan su faduwa kasa wanwar. Ba su da wata makama ko mafita, sai kawai su ka fake da ire-iren wadannan harkokin rashin kyautawa da rashin mutunci.
Maigirma Gwamna Ganduje ya bayyana cewar ya tabbatar su ‘yan Kwankwasiyya kawai sun yankewa kan su hukuncin huce haushinsu ne a kan ‘yan jam’iyyar APC da jama’ar gari saboda su tayar da hankulan jama’a dan su tsorata su su ki zuwa zaben da ke gabanmu na wannan shekarar ta 2019.
Gwamna ya na yi wa wadanda a ka zalunta a ka raba su da rayukansu ba gaira ba dalili, addu’ar Allah Ya jikansu da rahama. Ya na kuma yi wa wadanda su ka ji ciwo fatan samun lafiya da sauri.
Ya umarci jami’an tsaro da su yi duk mai yiwuwa wajen zakulo wadanda ke da hannu wajen wannan ta’asa da fatan a hukunta su daidai da laifukan da su ka aikata. Gwamnan ya sha alwashin ganin an hukunta duk wanda ke da hannu a wannan abin Allah Wadai.
Sa Hannun
Muhammad Garba,
Kwamishinan Yada Labarai Na Jihar Kano
21 ga Watan Fabrairu, 2019