Thursday, December 19, 2024
HomeHausaZamafara: Zargin karbar Nagoro ga Alkali

Zamafara: Zargin karbar Nagoro ga Alkali

Daga: Abubakar Sadeeq

Hakika duk wanda yake bibiyar labaran da mujallarmu ta Taskira Magazine ta ke wallafawa ya kwana da sanin cewa kwanakin baya ta wallafa wani labari mai take “ZAMFARA: ANA ZARGIN GWAMNA ABDULAZIZ YARI YA NA SHIRIN JIRKITA SAKAMAKO SHARI’A’ a cikin rubutun mun rawaito sahihin bayani da muka samu na yadda Mai Daraja Gwaman Yari ya aike ma Mai Shari’a ma kudan kudi ta hannun lawyansa da kuma Amininsa Liman Alhaji. Hakika a lokacin da labarin ya fita mutane da yawa sunyi ta tofa albarkacin bakin su, wasu suna cewa munyiwa Gwamna Kazafi, wasu suna cewa munyiwa Maishari’a Sharri dadai sauran batutuwa masu yawa da suka biyo baya.

A ranar Larabar nan da wuce 28th ga watan Nuwamba 2018, rana ce da Mai Shari’a Mukhatr Yusha’u ya sanya domin dawowa kutu a cigaba da shari’ar da Gwamnan Zamfara ya shigar ya gurfanar da Uwar Jam’iyyar sa ta APC da kuma Hukumar Zabe ta INEC, ya na so kotu ta tursasa Uwar Jam’iyya ta amince da Sunayen ‘yan takararsa ita kuma Hukumar Zabe ta karbi List din. Kamar yadda rahoto ya zo mana, bayan zaman kotun a wannan rana Mai Shari’a Mukhtar Yusha’u ya janyo hankalin lauyoyin da suke wajen cewa yana fuskantar matsin lamba sosai daga Jami’an Gwamnati akan shari’ar, haka kuma Maganganu na yawo akan cewa ana zarginsa da cewa ya karbi na goro daga Gwamnati, a saboda haka shi ba zai iya cigaba da yin wannan shari’ar ba zai mayarwa da Babbar Mai Shari’a File din domin a bawa wani ya cigaba. Gaba daya Lauyoyin da suke wajen daya bayan daya sunyi jawabai na karfafa gwiwa ga Mai Shari’ar tare da kawo masa misalai kala kala domin ya canja niyyarsa amma sam yaki yarda, wannan shine abun Hausawa suke cewa “ Duk abun da ka ga ya koro Bera ya fada Wuta, to Lallai ya fi Wutar Zafi’  Mai Shari’a Mukhtar ya nuna cewa shi Dattijo ne, sunansa ya baci gara ya tsira da mutuncinsa.

Dangane da yadda sakamakon wannan shari’a ya nuna cewa babu rana balle lokacin ci gaba da ita, mun samu rahoton cewa Gwamna da mukarrabansa sun dukufa wajen shirye-shiryen sauya Jam’iyya kafin lokaci ya karasa kurewa. Fatan mu dai Allah ya tabbatar da zaman lafiya a Jihar Zamfara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

FOLLOW US:

6,985FansLike
1,458FollowersFollow
553SubscribersSubscribe

Most Popular