Sunday, September 8, 2024
HomeHausaBudaddiyar Wasika Daga Hadakar kungiyoyin Matasa Masu Rajin cigaban jihar Kano Kan...

Budaddiyar Wasika Daga Hadakar kungiyoyin Matasa Masu Rajin cigaban jihar Kano Kan AGILE

Gamayyar Ƙungiyoyin Matasa Masu Rajin Kare Jihar Kano.

Sakamakon wata sanarwa da wasu daidaiku ke yi game da shirin nan na AGILE a Jihar Kano.

Gamayyar kungiyoyi Sun bi diddigi tare da tuntubar wadanda abin ya shafa, musamman Gwamnati da
jami’an shirin, da wasu daga cikin iyayen yaran sama da 800,000 dake Makarantun Gwamnati a Jihar Kano, da su kansu daliban, da malaman da ke ba da horon, da sauran masu ruwa da tsaki.

Haka kuma mun bibiyi ita kanta manhajar da ake horar da yaran, tare da sauran manhajojin sauran darussan sakandire, ba mu sami wani dalili da za a ce ta sabawa Addini, da al’adu ko kuma zamantakewarmu ba.

Don haka wannan batu kage ne mara tushe da muka kasa gane abinda masu yada shi ke burin cimmawa, a cigaban aľummar Jihar Kano baki daya.

A zurfafa bincikenmu, mun tabbatar cewa Gwamnatin Jihar Kano ta fara gudanar da shirin Agile tun shekarar 2021, tare da jihohin Borno,Katsina, Kaduna, Kebbi, Plateau da Ekiti, bayyanar alfanun da ke kunshe a cikin shirin a yanzu haka wasu karin jihohi sun sami nasarar shiga.

Kamar su Jihar Jigawa, Zamfara, Bauchi, Gombe, Yobe, Kogi, Niger, Kwara da sauransu.

Rawar da Bankin Duniya ke takawa kawai ita ce, shi ne ya ba da lamanin kudaden gudanarwa, wanda kuma za a biya cikin wasu shekaru nan gaba.

Mun bincika kuma mun tabbatar shirin AGILE ba shida wata alaka ta kusa ko ta nesa da Yahudawa, ba kamar yadda wasu yan amshin shata ke zuzuwa hakan ba.

Kuma dukkan al’umma suna ganin irin alfanun da wannan shiri ya kawo a makarantun sakandire na duk fadin Jihar Kano.

Wannan kungiya tamu tana kira ga dukkan jama’a da su bibiyi makarantun yankunansu.

Haka kuma iyaye su tuntubi ‘ya’yayensu, domin tabbatar da sahihiyar gaskiyar lamarin.

kofar jami’an wannan shiri, da ta mahukunta a bude take ko da yaushe, ga masu neman karin bayani, ko shawara, ko tattaunawa game da dukkan tsare-tsaren wannan shiri.

ofishin mu na hawa na uku, Gidan Murtala, Kofar Nassarawa,cikin Birnin Kano.

Muna shawartar al’umma da muguji yada jita -jita ba tare da bincike a kan ingancin labaran yanar gizo ba, musamman game da muhimmin kokari da Ma’aikatar Ilmi keyi wajen inganta rayuwar al’umma domin ci gaban Jihar Kano baki daya.

A madadin kungiyoyi kamar haka

Gamayyar kungiyoyin jahar Kano masu fafutukar samar daci gaba
Wanda suka hada da:

-Network For Youth Enlightenment And Development N-YED.

  • Association of Nigerian Women and Youths for Peace Advocates

-(ANWOPA)Kano chapter,

Youth-Mobilization by Media,

-Fighting Against–
-Women and Children Violation,Kano Youth Progressive Concern,

-Arewa Peace Ambassadors,-

-NACCRAN Kano State,

-ArewaYouth Innovative of Nigeria.

-Kano Progressive Mindset Forum.

-Kano State Network for youth Initiative.

-Arewa Youths Political Gladiators (AYPG).

-Kainuwa Youth Progressive Community Development.

-African Emancipation Movement(Kano Chapter).

-Arewa Students Forum,

Kungiyar-Daliban Nigeria Reshan jahar Kano

-KASYADREC(DRUGS ORG.)

Amb.Nura Abdullahi Saraki Babban Sakatare

A madadin: Gamayyar Ƙungiyoyin Matasa Masu Fafutukar Ganin ci Gaban Jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

FOLLOW US:

6,985FansLike
1,458FollowersFollow
553SubscribersSubscribe

Most Popular