Thursday, December 19, 2024
HomeHausaAl'ummar jihar Gombe, Jihar zasu Kalla ba Jam'iyya ba @Khamis Mailantarki

Al’ummar jihar Gombe, Jihar zasu Kalla ba Jam’iyya ba @Khamis Mailantarki

Daga Kabiru Getso

Dan takarar Gwamanan Jihar Gombe a tutar Jam’iyyar NNPP Hon KHAMIS Mailantarki ya bayyanna cewar Al’ummar jihar Gombe zasu yi mutum ne ba Jam’iyya ba.

Ya bayyanna hakanne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a ofishinsa,yace duba da Shekaru takwas da Jam’iyyar APC ta kwashe tana mulki amma babu wani abun a yaba da Gwamnatin ta samar yasa Al’ummar jihar daukar wannan matakin.

Mailantarki ya kara da cewar Yanzu lokaci yayi da Al’ummar zasu farka domin zabar wanda zai rike amanar Al’ummar jihar ta hanyar sauke nauyin da ya rataya a wuyan Shugaban, ta fuskar ayyukan cigaba da inganta rayuwar Al’umma.

Yace sanin kowane idan akayi waiwaye a baya lokacin ya yake Dan Majalisar Tarayya, yayi ayyuka wadanda suka zagaye dukkanin mazabun kananan hukumomin da ya wakilta,wanda hakan ne jama’a suke da yakinin zabarsa a matsayin Gwamnan jihar ta Gombe domin kawo nagartaccen sauyi.

Mailantarki ya kara da cewar Jam’iyyar NNPP a jihar Gombe farin jininta kullum kara bunkasa yake la’akari da irin manyan Mutanen da suke hijira suna komawa Jam’iyyar.

Yace Matasa Shaidane irin kokarin da ake wajen inganta rayuwar su Musamman ta fuskar Sha’anin wasanni inda jihar Gombe tana daya daga cikin jihoshin da ta samu zaratan ‘yan wasa da ake alfahari da su, kuma tsarinmu ne ke daukar nauyinsu har zuwa kasar wajen don samun horo na Musamman inji shi.

Mailantarki ya yabawa Al’ummar jihar Gombe bisa irin Goyon bayan da suke bashi tare da kira garesu da suci gaba da jajurcewa domin samun nasarar Jam’iyyar NNPP a matakai daban daban na jihar baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

FOLLOW US:

6,985FansLike
1,458FollowersFollow
553SubscribersSubscribe

Most Popular