Sunday, June 16, 2024
HomeHausaKakakin majalisar kasa ya dauki nauyin karatun wasu Dalibai a Kano

Kakakin majalisar kasa ya dauki nauyin karatun wasu Dalibai a Kano

Daga Kabiru Getso

Kungiyar Ma’aikatan Ofishin Kakakin majalisar kasa Femi Gberjabiamila (Gbaja Professinals Volunteers Network ) da hadin kwiwar Kungiyar Malaman gaba da sakandire na yankin Dawakin Tofa sun Dauki Nation Karatun daliban yankin har su 130 tun daga matakin firamare.

Shugaban ma’aikatan ofishin kakakin majalisar Hon Sunusi Garba Rikiji wanda ya wakilci kakakin majalisar ya bayyana cewar wannan tsari somin ta6i ne, domin zasu cigaba da aiwatar dashi a sassa daban daban dake fadin kasarnan.

Ya kara da cewar kakakin majalisar kullun zuciyarsa a bayyana take wajen daukar Nigeria a Matsayin dunkulalliyar kasa baki daya, shiyasa kullun yake kokarin aiwatar da shirin tallafawa karatun kananan yara a kowanne yankin kasarnan.

Shima a nasa jawabin shugaban karamar hukumar Hon Ado Tambai Gwa wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Garba Yusif Labour ya nuna farin cikinsa bisa wannan kabakin arziki da karamar hukumar Dawakin Tofa ta samu, inda ya bayyana gamsuwarsu da irin wannan gudummuwa da suka samu inda yaja hankalin Sauran al’umma masu rike da madafun iko da suyi koyi da wannan kyakkyawan tsari.

A karshe Hakimin Dawakin Tofa Alh Isma’il Umar Ganduje ya bayyana jin dadinsa bisa wannan abin alheri tare da fatan A’ummar da suka taru a wajen kaddamarwa sun koma gida lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

FOLLOW US:

6,985FansLike
1,458FollowersFollow
553SubscribersSubscribe

Most Popular