Daga Kaviru Getso
Shugaban karamar hukumar Birnin Kudu Hon Muktar Yusif Gogi ya bayyana cewa tuni Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin birinin kudu da Buji Hon Suraj Muhammad Kantoga ya yayi magana da ma’aikatar ayyuka ta kasa domin gina sabuwar gadar wacce ta lalace duba da yadda al’umma ke shan wahala sufuri a yankin.
Yace a satin nan ne aka turo ma’aikata domin su fara aikin hanyar tare da yin wata daban wacce al’ummar zasu fara wucewa kafin kammaluwar babbar gadar.
Kazalika Hon Muktar ya yabawa al’ummar yankin bisa hakuri da da’a da suke nunawa inda yace nan bada jimawa ba matsalar hanyar zai zama tarihi.
Hon Muktar ya yabawa Gwamnan jihar jigawa bisa hobbasa da yake wajan basu damar aikace aikace ga al’umma inda yace a karamar hukumar Birinin Kudu an amfana da ayyuka sama da guda dari tun bayan hawansa a kwana dari da suka gabata.
Ayyukan sun hada da kyaran masallatai, Samar da ruwan sha da inganta harkar lafiya tsaro da sauran ayyuka da dama.