Daga Abubakar Sadiq
Alƙalan da ke jagorantar wannan Shari’a su biyar sun shigo Kotu, sun zauna da misalin ƙarfe tara da minti goma sha biyu 09:12am.
Al’ummar jihar Zamfara, yau ba Acting CJN Ibrahim Muhammad Tanko ne ya jagoranci zaman Kotun ba, Mataimakin sa ne ya jagoranci zaman a yau.
Kuma ya bayyanawa Lauyoyi da mahalarta Kotun Shari’un da za su yankewa Hukunci a yau.
Daga nan ya baiwa Lauyoyin da ke kare kowane ɓangare dama, sun gabatar da kawunan su a gaban Kotun, kamar yadda Doka ta tanada.
Daga bisani jagoran Alƙalan biyar ya baiwa ɗaya daga cikin Alƙalan biyar Mace, damar fara karanta Hukuncin, kamar haka:
Jagoran Alkalan ya fara da cewa:
“Wannan shi ne Hukuncin kamar haka, Ƙuri’un da aka zubawa Ɗan-takarar Kujerar Gwamna na Jam’iyyar APC a babban zaɓen da ya gudana a wannan shekara ta 2019, wannan Kotun ta tabbatar da ba yi zaɓen fitar da gwanin Jam’iyyar APC a jihar Zamfara ba, kuma ta ba da damar saka Ɗan-takarar da ya yi na biyu a jihar Zamfara, a matsayin wanda zai hau kujerar Gwamnan jihar Zamfara, Hon.Bello Muhammad Matawallen Maradun, shi ne halattaccen Gwamnan jihar Zamfara”