Sunday, December 22, 2024
HomeHausaShugaba Buhari ya Tabbatar da goyon bayansa ga Takarar Gwamna Ganduje

Shugaba Buhari ya Tabbatar da goyon bayansa ga Takarar Gwamna Ganduje

A jiya Alhamis 31 ga Watan Junairu 2019, rana ce maimatukar tarihi a Siyasar jihar Kano a wannan zamanin mulkin maigirma Gwamna Ganduje, wadda za’a dade ba’a manta da ita ba, musamman a wannan gabar da zabe ya rage ‘yan kwanaki kadan. Babban muhimmun abun da ya faru a wannan rana shine ziyarar yakin Neman zabe da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo jihar Kano wadda akayi ta yada zantuttuka akan cewa ba zai zo ba.

Hakika al’ummar jihar Kano sun nuna halacci wajen yin tururuwa taren maigirma Shugaban Kasa run daga filin jirgin sama zuwa gidan maimartaba Sarkin Kano inda ya kai masa ziyarar bangirma da kuma neman sanya albarka. Shugaban Buhari tare da Gwamna Ganduje bayan sun kammala ziyara a Fadar Sarkin ne suka wuce zuwa filin wasa na Sani Abacha inda ake gabatar da taron gangamin neman zaben shugaban kasar; miliyoyin masoya sun yiwa Baba Buhari kyakkyawar maraba har ana rera wakoki “Baba Oyo yo”.

A jawabin Shugaba Buhari ya tabbatar da cewa Kanawa sun fi kaunarsa da mutanen Garinsu na Daura saboda yadda ya ga kauna ta zahiri a fili, daga karshen jawabinsa ya kama hannun Ganduje ya daga sama yace “Kanawa ga Gandujen Ku”.

Akwai mutane da yawa da suke adawa da gwamnatin Gwamna Ganduje, suna ta yada karya akan cewa Baba Buhari baya kaunar maigirma Ganduje da dai sauran surutai kala kala, yanzu kuma sai muji da abun da zasu fito kuma.

Nigeria dai ta tabbata ta Buhari, Kano kuma sai Ganduje.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

FOLLOW US:

6,985FansLike
1,458FollowersFollow
553SubscribersSubscribe

Most Popular