Daga Abubakar Sadiq
Kamar yadda jama’a su ka sa ni, a ranar Litinin da ta gabata, Gwamnatin Jihar Zamfara ta janye daya daga cikin karar da ta shigar akan turka-turkar Primary Election na Jam’iyyar APC kasancewar sun fuskanci Kotu zata kori karar saboda rashin Makama.
Akwai daya karar da Gwamnatin ke bibiya da take gaban Mai Sharia Mukhtar Yusha’u na State High Court, a inda Gwamna Yari ya gurfanar da Hukumar Zabe ta INEC da kuma Uwar Jam’iyyar APC, gwamnan ya na so Kotu ta tursasa Uwar Jam’iyya APC da Kuma INEC da su amince da list din ‘yan takarar da yake wajensa domin su zama cikakkun ‘yan takara a zaben 2019 dake gabato wa.
Akwai sahihin bayani da Taskira Magazine ta samu daga wani da bayaso a ambaci sunansa akan cewa Gwamna Yari ya aikewa alkalin Kudi Naira Miliyan 50 Cikin manyan jakunkuna guda biyu ta hannun Hadiminsa Liman Alhaji da kuma Lauyansa Barr. Sani Katu sai kuma Rtd. Justice Abdullahi Maikano wanda shi kawu ne ga alkalin.
Hakika wanna ya tabbatar da yunkuri da cuku-cuku da Gwamna ya ke yi na ganin ya samu nasara a zaman da kotu zata kara Yi a Ranar Alhamis 16 ga watan Nuwamba 2018.
Taskira Magazine tayi kokarin tuntubar maimagana dayawun Gwamanan Alh. Ibrahim Dosara domin ya bayar da ba’asi amma bai daga waya ba.
Muna fatan Allah ya kawo karshen wannan turka-turka.