Daga: Abubakar Sadeeq
Dangane da jita-jita da ake yadawa akan cewa Gamayyar ‘yan Takarar Gwamna ta G8 sun sun amince da sulhu ba gaskiya ba ne.
Maigirma Mataimakin Gwamna yayi karin haske a wani Dan karamin jawabi da yayi a gidansa dazu da rana, ya ambato cewa Mai Daraja Gwamna Abdulaziz Yari ya ziyarcesu domin neman gafara akan munanan kalamu da ambata akan su ‘Banza Takwas’.
Malam Wakkala ya cigaba da cewa a matsayinsa Na shugaba ya gane kuskuren da yayi ya nemi afuwa, shi yasa suka amsa masa cewa sun yafe masa, amma fa gwagwarmayar da suke yi akan ayi Damokaradiyya ta gaskiya ta barin al’umma su zabi abun da suke so ta na nan daram.
A karshe yayi kira da Jama’ar Jihar Zamfara da suyi watsi da Duk wani zance da ake yadawa.