Friday, December 20, 2024
HomeHausaZan Kafa hukumar Gudanar DA Aure, Sheik Badaru

Zan Kafa hukumar Gudanar DA Aure, Sheik Badaru

Daga Kabiru Getso

Tshon Dan Takarar Gwamnan jihar kano a jam’iyyar GPN kuma mai neman Takarar a jam’iyyar APC a kakar zaben 2023 Mai zuwa Badaruddeen Mu’azu wanda aka fi sani da Sheak Badaru Kano,ya bayyana cewa zai kafa hukumar gudanar da aure matukar ya zama Gwamnan jihar Kano.

Sheak Badaru Kano ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai, jim kadan bayan kammala Babban zaben shugabancin jam’iyyar APC na kasa.

Sheak badaru ya kara da cewa Aure ibada ce da take da matukar mahimmanci ga rayuwar al’umma don haka Wajibi ne Gwamnatoci su bada cikakkiyar kulawa a Sha’anin na auratayya.

Ya kara da cewa abin takaici ne kwarai matuka idan akayi la’akari da yadda aure take saurin mutuwa a cikin al’umma, ga kuma wahalhalu na al’ada da suka dabaibaye Sha’anin Auren.

Sheak Badaru kano yace matukar akayi kyakkyawan tsari to babu shakka za’a samu cigaba mai tasiri wajen inganta auratayya tsakanin al’umma.

Kazalika sheak badaru Kano Yayi kira ga sauran masu hannu da shuni da su cigaba da kokarin fitar da zakka yadda ya kamata domin rage radadin talauci da wahalar rayuwa da al’umma ke ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

FOLLOW US:

6,985FansLike
1,458FollowersFollow
553SubscribersSubscribe

Most Popular