Wednesday, May 29, 2024
HomeHausaSama da Matasa 150 sun Halarci Taron Tantance Jarumai na Film din...

Sama da Matasa 150 sun Halarci Taron Tantance Jarumai na Film din Baban Daji

Daga Abubakar Sadiq

Taron da aka gabatar dashi yau Litinin 28 ga watan Maris 2022 a filin wasa na Honey Badger dake Ku sa da Filin Jirgin sama na Malam Aminu Kano, ya samu halartar matasa daga ciki da wajen jihar Kano. Haka kuma taron ya samu halartar sababbi da tsofaffin Jarumai daga masana’antar Kannywood.
Fim din Babban Daji wanda kamfanin Taskira Media Limited ya shirya, ya kasance film ne mai Dogon Zango wanda ya ya kunshi labarin wasu matasa da su ka sami kansu a wani hali a lokacin da su ka he aiki a cikin wani Daji.
Jagoran masu tantancewar kuma Daraktan film din AGM Bashir ya yi kira ga matasa mahalarta tantancewar da su tabbatar sun yi rijista da hukumar tace finafinai ta jihar Kano domin shine mataki na farko na zama Jarumi a masana’antar Kannywood, daga karshe yayi fatan alheri ga matasan matansu da mazansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

FOLLOW US:

6,985FansLike
1,458FollowersFollow
553SubscribersSubscribe

Most Popular