Thursday, March 28, 2024
HomeHausaBabu Tantama Jam'yyar APC zata lashe zabe a Jihar Kano - Gov....

Babu Tantama Jam’yyar APC zata lashe zabe a Jihar Kano – Gov. Ganduje

Daga Aminu Dahiru

Mai girma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje (Khadimul Islam) ya jinjinawa Jama’ar Jihar Kano abisa yadda suka fito suka kadawa Jam’iyyar APC kuri’a a zaben da ya gaba na ranar Asabar 9 ga watan Maris 2019 cikin lumana da kwanciyar hankali.

Haka kuma ya jinjinawa Hukumar zabe ta INEC akan tsare-tsarensu da suka gabatar har aka kammala zabe cikin nasa duk da cewa daga baya, hukumar ta fito da bayani akan cewa zaben bai kammala ba saka makon wasu mazabu da aka soke wanda kuma ita hukumar ta saka ranar Asabar, 23 ga watan Maris 2019 za’a gabatar da zabe a daidaikun mazabun da aka soke.

Maigirma Gwamna yayi jawabin nan ne jim kadan da dawowarsa daga Abuja bayan ziyarar aiki ta yini daya da ya kai garin Abuja, ya cigaba da cewa yana cike da kyakkyawan yakini cewa al’ummar jihar Kano, zasu zabe shi duba da ayyukan cigaba da inganta tattalin arzikin jihar Kano da gwamnatin sa ta ke yi, haka ma da ayyukan raya kasa da aka fara kuma ake da niyyar karasawa idan gwamnati ta dawo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

FOLLOW US:

6,985FansLike
1,458FollowersFollow
553SubscribersSubscribe

Most Popular