Thursday, December 19, 2024
HomeHausaTALLAFIN PDP KWANKWASIYYA: YAUDARA KO SON ZUCIYA

TALLAFIN PDP KWANKWASIYYA: YAUDARA KO SON ZUCIYA

Daga Aminu Dahiru

Hausawa na cewa ‘Shure-Shure baya hana mutuwa’ hakika duk wani dan Nigeria ya kwana da labarin mummunan kayen da Jam’iyyar PDP ta sha a zaben da ya gabata na shugaban kasa, ‘yan majalisar Dattijai da kuma ‘iyan malisar tarayya, wanda Jam’iyyar APC ta samu gagarimar nasara a kasa musamman ma a Jihar Kano yadda ta bayar da tazarar kuri’a fiye da Miliyan Daya. Hakika wannan kaye ya wargatsa duk wani lissafin ‘yan kwakwasiyya wanda ya saka da dama daga cikinsu suka saduda domin sun san babu abun da zai canja a zaben Gwamna da ‘yan Majalisar Jiha da za’a yi nan gaba kadan.

‘Yan Kwankwasiyya sun fito da wata sabuwar yaudara, ta yadda suka fito da wani Sabon Form Mai Suna ‘PDP Kano State Kwankwasiyya Empowerment Programme 2019’ suna raba shi kyauta akan cewa za’a rabawa jama’a Tallafi Kyauta. A cikin Form din suna tambayar bayanai da ya hada da Cikakken Suna, Lambar Waya, Karamar Hukuma, Mazaba, Lambar Akwati har da Lambar Katin Zabe da kuma sauran bayanai. Abun tambaya anan shine me yasa sai yanzu za’a bijiro da wani rabon Tallafi? Kuma wane tallafi za’a bawa mutum da sai an dau Lambar Katin Zabensa? Wadan nan tambayoyi sun isa ga duk wani mai hankali ya tabbatar da cewa wannan cikakkiyar Yaudarace kawai da son zuciya ko kuma Sayen Kuri’a a fakaice, don haka muyi hattara.

Idan ana maganar Tallafi ya zama dole a yi jinjina ga Maigirma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje saboda tallafi dabam dabam da aka fito da shi wanda jama’a su ke ta amfana dashi kamar su: Tallafin Manoma Shinkafa da Alkama; Tallafin Masu Facin Taya; Tallafin Masu Gyaran Mota; Tallafin Masu Gyaran Waya; Tallafin Masu Gyaran Adaidaitasahu; Tallafin ‘Yan Shayi da dai sauransu. Hakika wadannan Tallafi dabam-dabam sunyi tasiri sosai akan matasan jihar Kano wanda yake bada tabbacin zasu fito kwansu da kwarkwata domin su zabi Gwamna Ganduje a karo na biyu.

Allah ya kaimu ranar zabe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

FOLLOW US:

6,985FansLike
1,458FollowersFollow
553SubscribersSubscribe

Most Popular