Daga Abubakar Sadeeq
Bayan dogon nazari na alkalai tare da dogayen jawabai sun kai matsayar yanke hukuncin amincewa da buƙatar lauyan Sen. Jaji kotu ta yi watsi da wannan ƙara.
Mutane da dama zasu yi mamakin mane ne hikimar janye wannan kara da Lauyan Jaji ya shigar. Wato abinda ke faruwa shi ne; Akwai zarge zarge da shakku na cewa idan aka cigaba da wannan shari’a za’a iya samun hukunci da mutane basu zato . Sannan kuma akwai yunkuri da Gwamna Yari yake so yayi amfani da shari’ar ya samu Court Order da zata tursasa Hukumar INEC ta karbi sunayen ‘yantakarar sa.
Duba da wannan yasa Lauyan jaji da sauran masu dafa masa baya, suka yanke shawarar janye karar.
Wannan zai ba INEC dama ta cigaba da yin tsayinta akan matakin da ta dauka na cewa APC ba tada ‘yan takara a Zamfara kamar yadda suka bayyana a farko. Domin babu wata kotu ta sama da ta basu wani umurni na cewa su karbi sunayen ‘yan takarar na APC.
